Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sabbin
Masarautun Kano da ya kirkiro za su cigaba da zama na
dindindin ko da ya bar karagar mulki.
Ganduje ya bayyana haka ne, a wajen taron ranar ma’aikata ta duniya da aka yi a filin wasa na jihar, inda ya ce an yi masarautun ne domin jama’ar jihar Kano, kuma ko ba su da gwamnati a hannu za su cigaba da addu’o’i.
Ya ce masarautun an yi su ne domin samar da hadin kai da ci- gaba da tarihi da kuma kara darajar sarautar gargajiya.
Kalaman Ganduje dais u na zuwa ne, bayan kalaman da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi game da masarautun Kano, inda ya ce akwai bukatar a sake yin nazari kan yadda aka karkasa masarautun jihar gida biyar.














































