Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta umurci dillalan magungunan aikin gona su janye maganin kwari samfurin ‘Sniper’ daga kasuwanni da manyan shaguna, sakamakon yadda mutane ke amfani da shi su na kashe kawunan su.
Daraktan hukumar Dakta Bukar Usman ya bayyana haka, a makarantar aikin gona da ke Ibadan, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamar da wani maganin Beraye ga manoman rogo mai suna ‘Lifeline’.
Ya ce samfurin ‘Sniper’ magani ne da aka yi shi domin aikin gona kawai ba don kashe kwarin cikin gida ba.
Dakta Bukar, ya kuma bukaci masu hada maganin da dillai su ba hukumar hadin kai don ganin an tsaida saida maganin a ko ina.
Ya ce ba wai an dakatar da saida maganin ba ne baki daya, amma za a takaita saida shi ga manoma kawai, ya na mai cewa duk magungunan aikin gona bai kamata a rika kai su gida ba.