Home Coronavirus Magance Coronavirus: Buhari Ya Bukaci Jihohi Su Bada Goyon Baya

Magance Coronavirus: Buhari Ya Bukaci Jihohi Su Bada Goyon Baya

403
0
Magance Coronavirus: Buhari Ya Bukaci Jihohin Su Bada Goyon Baya
Magance Coronavirus: Buhari Ya Bukaci Jihohin Su Bada Goyon Baya

Gwamnatin tarayya ta nuna rashin amincewa bisa sabanin da ake samu a matakan da ta ke dauka kan yaki da cutar Coronavirus da kuma matakan da wasu jihohi ke dauka.

Bayanin haka na zuwa ne jim kadan bayan gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar takaita zirga-zirga a Jihar Kano da mako biyu.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da gwamnonin jihohi ta yanar gizo, akan batun yaki da cutar COVID-19 da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma tsaro.

Shugaba Buhari ya ce, gwamnatin tarayya na tufka amma wasu jihohin na warwarewa, saboda haka wajibi ne jihohin su bada goyon bayan domin yaki da cutar.

Mai taimakawa shugaban kan harakokin yada labarai Garba Shehu ya ce, abin takaici ne a ce gwamnatin tarayya na daukar matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai.

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya amince da shawarwarin da malamai su ka ba shi, matakin da ya sa ya amince da yin Juma’a da kuma Idi.