Dubun wasu mutum uku da ake zargi da garkuwa da mutane a yankin Ossra-Irekpeni da ke kan kan hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja a Jihar Kogi ta cika, bayan da aka cafke su a maboyarsu.
Daya daga cikin mafarautan yankin, da suka sami nasarar kama su ya ce sai da suka yi musayar wuta tsakaninsu da masu garkuwar kafin su shiga hannu.
Ya ce mafarautan, tare da hadin gwiwar Shugaban Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogin, Samuel Omuya, ne suka yi wa dajin kawanya da yammacin ranar Laraba, bayan samun wasu rahotannin sirri kan maboyar bata-garin.
A cewarsa, hakan ne ya sa ’yan bindigar suka bude musu wuta, inda su kuma suka mayar da martani.
Ya kuma ce wasu daga cikin masu garkuwar sun tsere da harbi a jikinsu, yayin da kuma aka damka wadanda aka kama din ga jami’an tsaro da ke Lokoja, babban birnin Jihar.
Shugaban Karamar Hukumar Adavi, ya tabbatar da akama mutanen, inda kuma ya jinjina wa mafarautan kan kokarinsu wajen samun nasarar.
To sai dai duk kokarin da aka yin a jina ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Ovye Aya, ya ci tura.














































