Gwamnatin Jihar Katsina ta dawo da cigaba da amfani da layukan wayar salula da aka tsayar saboda dakile matsalar tsaro a wasu Kananan Hukumomin Jihar.
An dai dakatar da amfani da layukan ne a watannin baya, don yaki da ayyukan ta’addancin da ’yan bindigar da suka addabi Jihar.
A watannin baya ne dai wasu jahohin arewa maso yammacin kasar nan suka rufe layukan sadarwa a wani mataki na magance matsalar hare-haren ‘yan Bindiga.
A baya-bayan nan dai Jihar kaduna kaduna ta bude layukan, yayinda Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara shirin bude kafafen sadarwar.
You must log in to post a comment.