Home Labaru Kotu Ta Umarci Gwamnatin Buhari Ta Yi Bayanin A Kan Bashin Dala...

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Buhari Ta Yi Bayanin A Kan Bashin Dala Miliyan 460 Na Aikin CCTV

85
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci gwamnatin
Shugaba Buhari ta yi bayani a kan yadda ta yi da dala miliyan
460 da aka karɓo bashi daga kasar China, domin ta kafa
kyamarar CCTV a birnin Abuja, aikin da aka ce ba a yi ba
kuma ba a san yadda aka yi da kuɗin ba.

Haka kuma, kotun ta umarci Gwamnatin Buhari ta gaggauta shiga shafukan jaridu ta bayyana adadin yawan kuɗin da aka maida a matsayin biyan bashin, idan har an biya ko an fara biya.

Kotun, ta Kuma nemi Gwamantin Buhari ta bayyana sunayen kamfanonin da aka ba kwangilar, da sunayen ‘yan kwangilar da kuma inda aikin ya tsaya.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya bada umarnin, a matsayin hukuncin da ya yanke na wata ƙara da aka shigar ta haƙƙin neman bayani daga gwamnati, wanda ‘yan Niujeriya ke da ‘yancin su nemi ta yi masu.

Ƙungiyar Rajin Hana Rashawa ta SERAP ce ta shigar da Gwamnatin shugaba Buhari ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.

Leave a Reply