Akalla likita 17 ne suka kamu da cutar Coronavirus a babban asibitin cutar kansa na kasar Masar.
Hukumomin Masar sun tabbatar wa ‘yan jarida cewa an killace likitocin ne bayan sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna sun harbu da cutar coronavirus.
Kamuwar likitocin na haifar da fargabar yiwuwar ma’aikatan jinya a asibitoci sun kamu da cutar ta COVID-19.
Cutar coronavirus ta kama mutum fiye da 1,000 a kasar Masar, inda ta kashe mutum 66.
Annobar cutar a fadin duniya ta tilasta wa gamnatoci rufe makarantu, da ma’aikatu da kamfano da wuraren ibada da kasuwani da harkokin da suka shafi taron jama’a.
Kawo yanzu cutar ta kama fiye da mutu miliyan daya a duniya, baya ga dubban da suka mutu. Kazalika daruruwan dubban mutane sun warke daga cutar, wadda ake kokarin samo mata magani.