Home Labaru COVID-19 Ka Iya Jefa Duniya Cikin Yunwa – MDD

COVID-19 Ka Iya Jefa Duniya Cikin Yunwa – MDD

425
0
Annobar COVID-19 na barazana ga bangaren aikin noma musamman a nahiyar Afirka.
Annobar COVID-19 na barazana ga bangaren aikin noma musamman a nahiyar Afirka.

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ce annobar cutar coronavirus ka iya jefa kasshen duniya cikin karancin abinci.

Ta yi gargadi cewa annobar na barazana ga samar da wadataccen abinci, duba da irin illar da cutar ke iya yi wa bangare noma musamman a nahiyar Afirka.

WFP ta ce yayin cutar ke ci gaba da yadaduwa, za a wayi gari abincin da ake da shi jibge a yanzu ya kare, lamarin da ka iya jefa mutane a wasu kasashe cikin rashin kudin sayen abinci.

Jami’an Hukumar Samar da Abinci ta MDD na saukar da kayan abinci a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.

Ta kara da cewa bangaren sufuri ma na fuskantar matsala, wanda ka iya kawo cikar wajen isar da abinci ga wasu kasashen duniya.