Home Labarai Legas Za Ta Yi Wa Mazauna 10m Rajista A Wata 5

Legas Za Ta Yi Wa Mazauna 10m Rajista A Wata 5

371
0

Gwamnatin Jihar Legas, ta ce za ta yi wa mazauna jihar miliyan 10 rajistar katin shaidar zama ‘yan jiha, domin tarawa a rumbin adana bayanan jihar daga yanzu zuwa karshen shekara ta 2022.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka, a wajen bikin sake kaddamar da fara aikin bada katin shaidar zama dan jihar da ta fara, wanda ya ce shi ne irin sa na farko a Yammacin Afirka gaba daya.

Sanwo-Olu, ya ce Hukumar yi wa mazaunan Rajista ta Jihar wato LASRRA, yanzu haka ta yi wa mutane miliyan shida da rabi rajistar, kuma ta na fatan kara yi ma wasu miliyan goma kafin karewar shekara ta 2022.

Hukumar LASRRA dai an kirkiro ta ne tun zamanin gwamnatin tsohon Gwamnan jihar Babatunde Raji Fashola, da zummar zamowa ma’adanar tara bayanan al’umma domin tsara jihar da kasafi daidai da bayanan da ta tattara.

Sake kaddamar da tsarin da Gwamna Sanwo ya yi a yanzu, ya ce ya yi shi ne domin rungumar canji mai amfani, da kuma yin kafada da kafada da kasashen da su ka cigaba da Gwamnatin sa ke yi.

Leave a Reply