Gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar ta ce ta kama wani da take zargin ɗan leƙen asirin Faransa da ke zaune a ƙasar.
Kafar talabijin na ƙasar Tele Sahel ya ruwaito cewa wanda ake zargin, mai suna Marius Barcea, ya shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba ranar 12 ga watan Nuwamba a hanyar amfani da fasgo na ƙasar Romania, amma kwana guda bayan shigar sa ƙasar aka kama shi.
Kafar talabijin ba ta yi wani ƙarin bayani ba kan mutumin da aka kama.
Wani shafi mai wallafa labarai kan ayyukan gwamnatin mulkin sojoji a Nijar da Mali da kuma Burkina Faso AES, ya kwatanta kama Barcea a matsayin wani koma baya ga Faransa.
Kamen yana ƙara nuna zarge-zarge da gwamantin Nijar ɗin ta sha yi wa Faransa, wanda ta ce tana son wargaza ƙasar da kuma janyo ruɗani a faɗin yankin Sahel.
AES ya ce duk da Faransa ta sha musanta zarge-zargen, amma ana ƙara samun hujjoji da ke nuna cewa Paris ɗin na yaƙin sunkuru kan Nijar, ta hanyar yaɗa labaran karya da kuma sauran abubuwa.