Home Labaru Lawan Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Borno Karo Na 4 A Jere

Lawan Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Borno Karo Na 4 A Jere

305
0

Majalisar dokoki ta jihar Borno, ta zabi Abdulkarim Lawan a
matsayin shugaban majalisar ta 10.

Abdulkarim Lawan dai shi ne tsohon kakakin majalisa ta tara, kuma ya kasance ya na shugabantar majalisar tun a majalisa ta shida.

Magatakardan majalisar Jidayi Mamza, ya ce Majalissar ta samu sako daga mai girma gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, inda ya bukaci ta gudanar da zaman ta na farko, bisa la’akari da ikon da aka ba shi a sashe na 105 karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulki na shekara ta 1999.

Majalisar, ta kuma zabi tsohon mataimakin kakakin majalisar Abdullahi Musa daga mazabar Askira Uba a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

A jawabin sa na karramawa jim kadan bayan rantsar da shi, Abdulkarim Lawan ya yaba wa ‘yan majalisar bisa sake zaben shi da su ka yi, sannan ya bukaci sabbin ‘yan kwamitin da aka kaddamar su kara matsa kaimi tare da hada hannu da bangaren zartarwa domin kawo sauyi a jihar ta fuskar ilimi da samar da abinci da tsaro da dai sauran su.

Leave a Reply