Home Labaru Bana Babu Hawan Babbar Sallah A Masarautar Zazzau

Bana Babu Hawan Babbar Sallah A Masarautar Zazzau

1
0

Masarautar Zazzau ta bada sanarwar cewa ba za a gudanar da
hawa ba yayin Babbar Sallah mai zuwa.

A wata sanarwa da masarautar ta fitar, ta ce hakan zai faru ne sakamakon tafiya aikin Hajjin da Sarkin Zazzau zai yi domin sauke farali.

Sanarwar ta cea ba za a yi hawan Babbar Sallah ba kamar yadda Mai martaba Sarkin Zazzau ya saba jagoranta a duk shekara.

Ta ce Mai martaba Sarkin Zazzau ya na yi wa kowa fatan Alhairi, da fatan za a cigaba da yin addu’o’i domin samun cikakken zaman lafiya a Nijeriya baki ɗaya.