Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kara wa babban
hafsan sojin kasa na Nijeriya Taoreed Abiodun Lagbaja girma
zuwa mukamin Laftanal Janaral mai tauraro uku.
Tinubu tare da mataimakin sa Kashim Shettima ne su ka Makala wa babban hafsan sabon mukamin a kafadar kakin soji a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Janar Lagbaja wanda daga bisani ya isa helkwatar rundunar sojin, inda aka gudanar da wata kwarya-kwaryar liyafa domin taya shi murna, ya mika godiyar sa ga mayakan Nijeriya, sannan ya nemi su kara jan damara domin ci-gaba da fuskantar kalubalen tsaron da ke damun Nijeriya
Sojojin, wadanda babban hafsa mai kula da manufofi da tsare- tsare Manjo Janaral Abdulsalam Ibrahim ya yi magana a madadinsu, sun yi alkawarin goyon bayan babban hafsan domin haka ta cimma ruwa.