Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya
koka da yadda ‘yan majalisar tarayya ke samun albashin da
bai taka kara ya karya ba.
Sanata Akpabio, ya ce kudaden da ‘yan majalisar ke samu ba su isar su wajen kula da yawan bukatun da su ke samu daga mazabu nsu.
Akpabio ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke maida martani a kan kudirin da Abdulrahman Kawu Suleiman na jam’iyyar NNPP daga jihar Kano ya dauki nauyi, a kan bukatar dakatar da kungiyar kwadago ta Nijeriya daga shiga yajin aikin da ta ke shirin yi.
Sanata Akpabio, ya ce ya aminta da cewa jama’a su na cikin wani hali tun bayan cire tallafin man fetur, sai dai ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su kara hakuri yayin da gwamnati ke tsara matakan rage masu radadin da su ke ciki.
Sanata Kawu Sumaila, ya ce yajin aikin da ake shirin farawa zai gurgunta tattalin arzikin kasa ta hanyoyi da dama, domin a cewar sa, yajin aikin zai janyo kulle makarantu kuma masu motocin haya za su daina aiki ya kuma janyo rufe kasuwanni da asibitoci da sauran su.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya koka da yadda ‘yan majalisar tarayya ke samun albashin da bai taka kara ya karya ba.