Home Labaru Kwankwaso Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu A Paris

Kwankwaso Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu A Paris

84
0

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u
Musa Kwankwaso, ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban
kasa Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunan ta, ta ce mutanen biyu sun shafe tsawon sa’o’i da dama su na tattaunawa.

Duk da cewa babu cikakken bayani game da abin da tattaunawar ta ƙunsa, amma ana ganin cewa ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnatin da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu ba.

Har yanzu dai zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai yi bayani dalla-dalla a kan yadda gwamnatin shi za ta kasance ba, amma ya na ƙoƙarin ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply