Home Labaru Ilimi Gwamnatin Tarayya Ta Bada Lasisin Bude Jami’ar Koyo Daga Gida Da Karin...

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Lasisin Bude Jami’ar Koyo Daga Gida Da Karin Wasu 37

1
0

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Lasisin Bude Jami’ar Koyo
daga Gida Da Karin Wasu 37, biyo bayan wani zama na
musamman da Majalisar Zartarwar ta kasa ta yi a Abuja.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana wa manema labarai haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jim kadan bayan wani taron gaugawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Adamu Adamu ya kara da cewa, kawo yanzu sabbin Jami’o’in sun kai adadin 72 da gwamnatin Buhari ta bada lasisin su tun daga shekara ta 2015.

Sai dai Ministan bai bayyana sunayen jami’o’in ba, amma ya ce daya daga cikin su jami’a ce ta yanar gizo, wadda ita ce irin ta ta farko mai zaman kan ta a Nijeriya mallakin wata mata daga jihar Bauchi.

Ya ce ana sa ran Jami’ar za ta dauki nauyin mata Musulmi ‘yan Arewa da ba su so, ko kuma wadanda aka hana shiga Jami’o’in da ake da su domin yin karatu.