Home Labaru Labarun Ketare Kwace Mulki: Taliban Ta Sanar Da Afuwa Ga Ilahirin Jami’An Gwamnatin Afghanistan

Kwace Mulki: Taliban Ta Sanar Da Afuwa Ga Ilahirin Jami’An Gwamnatin Afghanistan

61
0
Taliban-Afghanistan-War

Kungiyar Taliban sun sanar da yin afuwa ga illahirn ma’aikatan gwamnatin kasar Afghanistan, tare da yin kira a gare su da su koma bakin aiki kwanaki biyu bayan kwace mulki daga hannun gwamnatin Ashraf Ghani.

A sanarwar da ta fitar safiyar yau, Taliban ta ce bai kamata ma’aikatan gwamnati su nuna wata fargaba ba, domin kuwa ba abin da zai faru da su a karkashin sabon mulkinsu.

Tun a yammacin Lahadin da ta gabata Taliban ta mamaye birnin Kabul yayinda Shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga kasar inda a jiya litinin kungiyar ta tabbatar da kammala kwace iko da kasar bayan fayafayan bidiyon da suka nuna jami’anta rike da fadar gwamnati.

Duk da cewa Taliban ta bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankulansu baya ga shan alwashin kin daukar fansa kan duk wani jami’I da a baya ya taimakawa gwamnati ko dakarun kasashen ketare a kokarin yakarta, har yanzu jama’a na ci gaba da tururuwa don gujewa mulkin kungiyar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ma’assasin kungiyar ta Taliban Abdul Ghani Baradar ya bukaci mayakan kungiyar da kada su kaucewa dokoki da ka’idojin da suke kai bayan kwace Kabul.