Home Labaru Kasuwanci Dokar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Zuba Jarin Da Ya Kai Dala...

Dokar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Zuba Jarin Da Ya Kai Dala Biliyan 50 – Buhari

53
0
Kudurin Man Fetur

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Nijeriya ta yi asarar zuba jarin da ya kai Dala biliyan 50 a cikin shekaru 10 da su ka gabata, saboda rashin sake fasalin dokar man fetur da iskar gas da ya sanya wa hannu a wannan makon.

Yayin da ya ke jawabi a wajen bikin sanya hannu a kan dokar a fadar sa da ke Abuja, Buhari ya ce tsaikon da aka samu wajen yin sabuwar dokar ya haifar da matsala wajen ci-gaban tattalin arzikin Nijeriya.

Shugaba Buhari, ya danganta matsalar da aka samu daga gwamnatocin da su ka gabata, wadanda su ka kasa samar da yanayi mai kyau wajen amincewa da sabuwar dokar da ta kwashe kusan shekaru 20 a gaban majalisa.

Ya ce sun fahimci cewa, gwamnatocin da su ka gabata na da masaniyar alherin da ke tattare da sabuwar dokar, wadda za ta bada damar gudanar da harkokin Mai kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya, amma su ka kasa maida hankali a kai saboda wasu dalilai.

Shugaba Buhari, ya ce tsaikon ya maida hannun agogo baya dangane da ci-gaban tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar zuba jari.