Home Labaru Kuskure: Ana Zargin Jirgin Saman Soji Da Buɗe Wa Jirgin Ruwan Farar...

Kuskure: Ana Zargin Jirgin Saman Soji Da Buɗe Wa Jirgin Ruwan Farar Hula Wuta A Ribas

104
0
Marine Police

‘Ƴan sandan ruwa a garin Bonny na Jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya sun soma bincike kan zargin da ake yi wa wani jirgin soji na buɗe wuta ga wani jirgin ruwan ɗaukar kayayyaki.

Rahotanni sun ce jirgin na ɗauke da kayan abinci da sauran abubuwa inda yake hanyar sa ta zuwa garin Bonny daga tashar ruwa ta Nembe-Bille da ke Fatakwal.

Awwal Rufai, wanda ke cikin jirgin ruwan a lokacin da lamarin ya faru ya shaida cewa lamarin ya faru ne a tsibirin Dutch da ke Okrika kuma har an harbe mutum biyu, cikin waɗanda aka harba har da Awwal ɗin.

Auwal y ace shi a ɗan yatsa harsashin ya same shi sai dai ɗayan mutumin a ƙwabri harsashin ya same shi, yayin da Sauran yaran da ke cikin jirgin sun yi tsalle sun faɗa ruwa.”

Jami’in ɗan sandan da ke kula da yankin ruwan Bonny, SP Solomon Adeniyi ya shaida wa BBC cewa sun samu rahoto kan wannan lamarin kuma tuni suka fara bincike.