Home Labaru Kungiyar Can Ta Caccaki Kungiyoyin Musulmai A Jihar Taraba

Kungiyar Can Ta Caccaki Kungiyoyin Musulmai A Jihar Taraba

77
0

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN reshen jihar Taraba, ta ce ita za ta sake zaben wanda zai zama gwamnan jihar saboda yawan mabiyan ta.

CAN dai ta soki mlamirin majalisar Musulmai ta jihar Taraba da kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC bisa ikirarin da su ke yi cewa ana muzguna wa Musulmi a jihar.

Kungiyar CAN, ta ce ko Musulmai su yarda ko kada su yarda su ne marasa rinjaye a jihar Taraba, kuma ba za su taba yin nasara a zabe ba.

Shugaban kungiyar CAN na jihar Taraba Rabaren Isaiah Magaji ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce tuhume-tuhumen da majalisar Musulmi da MURIC ke yi farfaganda ce, kawai su na son yi wa Kiristocin jihar barazana ne alhalin su ne mafi rinjaye.

Rabaren Magaji ya kara da cewa, kungiyar CAN ta na da ikon yin irin abin da Gwamna El-Rufa’i yayi a Kaduna na zaben mataimaki Musulmi, amma su na hakuri da Musulmai kawai don zaman lafiya.