Home Labaru ‘Yan Bindiga Da Ake Zargi IPOB Ne Sun Kashe ‘Yan Sanda Uku...

‘Yan Bindiga Da Ake Zargi IPOB Ne Sun Kashe ‘Yan Sanda Uku A Enugu

73
0

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ne sun kashe jami’an ‘yan sanda uku tare da raunata wasu biyu a jihar Enugu.

Maharan dai sun hari ne a kan wani shingen bincike na ‘yan sanda da ke Enugu a ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sandan ya shaida wa manema labarai.

Jami’in, ya ce sun rasa jami’ai uku, yayin da wasu biyu sun samu raunuka.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki tabbatar da adadin wadanda su ka mutu, ya na mai cewa har yanzu ba su da cikakkun bayanan da su ka shafi lamarin, amma an fara farautar ‘yan bindigar.