Home Labaru Majalisar Dattawa Za Ta Dauki Mataki A Kan Kudin Karatun Jami’a

Majalisar Dattawa Za Ta Dauki Mataki A Kan Kudin Karatun Jami’a

32
0

Majalisar dattawa ta na kokarin magance matsalar da za a iya fuskanta a harkar ilmin Boko sakamakon tashin kudin makaranta a jami’o’i.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce za su yi bakin kokarin su wajen ganin an hana kudin karatun jami’a tashi.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, Ahmad Lawan ya ce ya zauna da jagororin gamayyar kungiyar dalibai na yankin arewa.

Sanata Ahmad Lawan, ya ce ya saurari korafin matasan, musamman ganin yadda ake neman kara kudin karatu a wasu jami’o’in da ke yankin Arewacin Nijeriya a wannan yanayi.

Ya ce za su yi wani abu a kan lamarin, duba da muhimmancin ilmi, ya na mai shan alwashin cewa ba za su bari a samu matsala a bangaren karatu ba.