Home Labaru Kuma Dai: Kwastam Ta Kori Jami’inta Da Buhari Ya Karrama Saboda Ƙin...

Kuma Dai: Kwastam Ta Kori Jami’inta Da Buhari Ya Karrama Saboda Ƙin Karɓar Rashawa

329
0

Hukumar Yaki da Fasa-kwauri ta Nijeriya, ta sanar da korar wani jami’in ta mai mukamin mataimakin shugaba Aminu Dahiru, tare da tilasta ma wani jami’in Bashir Abubakar yin murabus. 

ACG Bashir Abubakar dai shi ne jami’in da Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamawa a shekara ta 2019, saboda kin karbar toshiyar baki na Dalar Amurka dubu 412 kamar yadda rahotanni su ka ambato.

A cikin wata Sanarwa da kakakin hukumar Joseph Attah ya fitar, ta ce ‘yan kwamitin zartarwa na hukumar sun amince da wannan matakin da ya dace da tsarin yi wa hukumar garambawul.

An dai kori jami’an biyu ne bayan samun su da laifin sakaci a watan da ya gabata, kamar yadda binciken da kwamitin ladabtarwa da aka kafa ya bayyana.

An dai tuhumi ACG Aminu Dahiru da hannu a badakalar fasa-kwaurin manyan motoci 295 dauke da man fetur a shekara ta 2019, yayin da aka zargi Bashir Abubakar da laifin bada umarnin kai samame a rumbun ajiyar shinkafa ‘yar gida, a kokarin sa na gano shinkafar waje a rumbunan ajiyar wani fitaccen mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina.