Home Labaru Artabu: Dakarun Soji Sun Kashe ‘Yan Bindiga A Benue, Sun Samo Makamai

Artabu: Dakarun Soji Sun Kashe ‘Yan Bindiga A Benue, Sun Samo Makamai

228
0
Sojoji Sun Kashe Mahara Sama Da 100 A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina

Dakarun rundunar sojin Nijeriya, sun kashe wasu da ake zaton ‘yan bindiga ne tare da kwato makamai.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na helkwatar tsaron Nijeriya Manjo Janar John Enenche ya fitar, ya ce dakarun Operation Whirl Stroke ne su ka yi nasarar kashe ‘yan ta’addan.

Enenche, ya ce an kaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri, inda dakarun su ka dauki mataki a kan ‘yan bindigar da aka alakanta da kashe-kashe a Makurdi. Ya ce yayin arangamar, dakarun sun sha kan ‘yan bindigar, sannan aka kashe daya daga cikin su, yayin da wasu da dama su ka tsere da raunin bindiga.