Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya: Yawaitar Amfani Da Gishiri Na Haifar Da Barazana Ga...

Kula Da Lafiya: Yawaitar Amfani Da Gishiri Na Haifar Da Barazana Ga Lafiyar Dan Adam

449
0

Wata kwararriyar likita Dakta Onyekachi Onubogu ta ce, yawan amfani da sinadarin dandanon gishiri na haifar da mummunar barazana ga lafiyar al’umma.

Dakta Onubogu ta shawarci ‘yan Nijeriya su rika sassauta amfani da sinadarin gishiri, domin ta ce yawaita amfani da gishiri na haifar da lalacewar Hantar dan Adama.

Kwararriyar Likitar ta bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da wani sabon sinadarin dandanon dunkulen Terra da ya gudana a Legas.

Ta ce yawaitar amfani da sinadarin dandano da kuma gishiri su na haifar da barazana ta rashin lafiyar Koda da kuma cutar hawan jinni, soboda haka kada mutane su shagala da son jin dandano a harshen su, domin kula da lafiya su.

Haka kuma ta yi gargadi al’umma su rika yawaita shan ruwa a kai a kai domin yana wanke duk wasu gurbatattun sunadarai da su ke makalewa a Hanta da Kodar jikin dan Adama.