Home Labaru Zato: Wasu Kasashe Ba Su Son Taimakawa Nijeriya Ne Saboda Tunanin Ta...

Zato: Wasu Kasashe Ba Su Son Taimakawa Nijeriya Ne Saboda Tunanin Ta Na Da Ariziki- Buhari

363
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, wasu daga cikin kasashen da suka cigaba basa son taimakawa Nijeriya saboda su na tunanin kasa ce mai arziki.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya bayyana haka a lokacin karbar takardun fara aiki na jakadun kasashe uku da suka hada da Indiya, Kuwait da Namibia da ya gudana a Abuja.

Shugaba Buhari ya tabbatarwa jakadan Kuwait, Al Bisher, cewa, sa Nijeriya cikin jerin kasashen duniya masu arzikin man fetur,wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin kungiyar kasashen duniya masu zarkin man fetura na duniya OPEC.

Buhari ya ce goyon bayan wasu daga cikin manufofin kungiyar ta OPEC a wasu lokutan, na hana kasashen da suka cigaba taimakon Nijeriya bisa tunanin cewa ta mai arziki ce.

Leave a Reply