Tsohon Ministan shari’a Malam Abubakar Malami zai fuskanci wani kwamitin bincike kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Wata majiya ta ce kwamitin da ke da alhakin ladabtar da Ma’aikatan shari’a ne ya gayyaci Abubakar Malami, bayan korafin da iyalan Kanar Sambo Dasuki su ka rika aikawa zuwa gaban kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya.
Iyalan tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki, su na karar Abubakar Malami ne bayan wasu kalamai da ya yi a gidan jarida a matsayin hujjar gwamnati na tsare Sambo Dasuki.
Gwamnatin Nijeriya dai ta ki sakin Sambo Dasuki duk da umarnin da kotuna su ka bada cewa a bada belin sa, inda Malami a lokacin ya na Minista ya tubure cewa laifin da ke kan Sambo Dasuki ba zai bari a kyale shi ba.
Malami ya ce, Kanar Sambo Dasuki ya na da hannu a mutuwar mutane sama da dubu 100 a Nijeriya, a lokacin mulkin Jonathan, don haka bai dace a kyale shi ya kubce wa hukuma saboda wani umarnin kotu ba. Hakan ya sa Iyalan Sambo Dasuki su ke so kungiyar ta hukunta Malami da laifin saba wa dokar aiki da kuma taka dokokin kasa da tsarin mulkin Nijeriya a lokacin ya na ofis.
You must log in to post a comment.