Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce Ofishin Antony Janar kuma Ministan Shari’a ya na da karfin ikon da doka ta ba shi na karbe shari’a daga hannun ta ya maida karkashin ofishin sa.
Kakakin Yada Labarai na hukumar EFCC Tony Orilade ya bayyana haka a Abuja.
Orilade ya yi raddi ne game da maganganun da ake yi a kan yadda EFCC ta bayyana wa Babbar Kotun Tarayya sanarwar janye hannu daga shari’ar da ta gurfanar da Sanata Danjuma Goje.
Hukumar EFCC dai ta maka Sanata Goje Kotu shekaru takwas da su ka gabata, bisa zargin sa da wawure naira bilyan 25 daga baitilmalin jihar Gombe a lokacin da ya yi gwamnan jihar tsawon shekaru takwas.EFCC ta yanke shawarar janyewa daga shari’ar ne kwana daya bayan da Goje ya bayyana janye wa Sanata Ahmed Lawan daga takarar Shugabancin Majalisar Dattawa.