Home Home Ku Zarge Ni Idan Har Miji Na Ya Gaza Cika Alkawuran Da...

Ku Zarge Ni Idan Har Miji Na Ya Gaza Cika Alkawuran Da Ya Dauka -Titi Atiku

80
0
Uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Hajiya Titi Atiku Abubakar, ta shaida wa daukacin matan Nijeriya cewa, ita za su zarga idan har mijin ta ya gaza cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zaben sa idan ya zama shugaban kasa.

Titi Abubakar ta kuma yi alkawarin cewa, idan Atiku ya zama shugaban kasa ba zai maida yankin kudu maso yamma saniyar ware ba, inda ta yi nuni da cewa, kada wa Atiku kuri’ar su tamkar zaben dan yankin su ne.

Uwargida Titi ta bayyana haka ne a birninAbeokuta, a wani taro da ta yi da matan jihar Ogun, inda ta ce idan aka zabi Atiku a matsayin shugaban kasa za ta zama matar shugaban kasa ta farko da ta fito daga kabilar yarbawa.

Ta ce ta na da yakinin cewa, idan har aka zabi Atiku zai iya kawar da talauci da magance kalubalen rashin tsaro a Nijeriya.