Home Home Awanni 72 Da Ficewa Daga Tafiyar Tinubu Da APC, Naja’atu Muhammad Ta...

Awanni 72 Da Ficewa Daga Tafiyar Tinubu Da APC, Naja’atu Muhammad Ta Ziyarci Atiku

112
0
Sa’o’i 72 bayan ficewa daga jam’iyyar APC, fitacciyar ‘yar siyasa Hajiya Naja’atu Muhammad ta ziyarci Atiku Abubakar a gidan sa da ke Abuja, inda ta sha alwashin yin gamayya da shi.

Sa’o’i 72 bayan ficewa daga jam’iyyar APC, fitacciyar ‘yar siyasa Hajiya Naja’atu Muhammad ta ziyarci Atiku Abubakar a gidan sa da ke Abuja, inda ta sha alwashin yin gamayya da shi.

Har yanzu dai ba a tabbatar da ko ta shiga cikin jam’iyyar PDP ba, ko kuma kawai zallar goyon bayan takarar Atiku Abubakar ta ke yi a zaben shekara ta 2023.

Kakakin kwamitin yakin zaben Atiku da Okowa Sanata Dino Melaye ya tabbatar da cewa, Hajiya Naja’atu Muhammad ta ziyarci Atiku Abubakar da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Sanata Dino Melaye, wanda aka hango a cikin hoton ziyarar tare da Naja’atu Mohammed da Atiku, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yar fafutukar za ta yi magana a kan lamarin ne a lokacin da ya dace.

Leave a Reply