
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, ta soki lamirin jam’iyyar Labour da dan takarar ta Peter Obi a kan rashin shirya wa karar da aka shigar ta kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A ci-gaban zaman kotun, daya daga cikin manyan lauyoyin da ke cikin tawagar lauyoyin masu shigar da kara Emeka Okpoko, ya nemi gabatar da takardun zabe a matsayin shaida a gaban kotun, amma an ce ba a gabatar da takardun yadda ya kamata ba kuma ba a shirya su a gaban kotun ba.
Don haka kotun ta dage sauraren karar na tsawon mintuna 10, sannan ta bukaci tawagar lauyoyin ta sake gabatar da jadawalin takardun kamar yadda aka tanadar da rahoton gabanin sauraren karar, amma duk da haka bayan kotun ta dawo tawagar lauyoyin ta kasance cikin rashin tsari.
Cikin rashin jin dadi, kwamitin mutane biyar na alkalan kotun a karkashin jagorancin Haruna Tsammani, ya shawarci masu shigar da karar su nemi a dage zaman su domin su tsara takardun su yadda ya kamata.
Alkalan sun bayyana abin da aka yi a matsayin bata lokaci, inda su ka ce lauyoyin masu shigar da karar sun raina muhimmancin aikin da ya kamata su yi.













































