Kotun ƙoli da ke birnin London, ta ce ‘yan Nijeriyar da ke son
shigar da ƙarar kamfanin man fetur na Birtaniya Shell sun
makara.
Mutanen, waɗanda ke yankin Neja Delta dais u na zargin kamfanin Shell da lalata masu muhalli bayan malalar man fetur a yankin fiye da shekaru 10 da su ka gabata.
Lauyoyin da ke wakiltar al’ummar yankin akalla dubu 30, sun ce malalar mai a yankin ya haddasa gurɓacewar ƙasa da rafuka, lamarin da ya janyo cikas ga fannin noma da kamun kifi da gurɓata ruwan sha da wuraren ibada a yankin.
A shekara ta 2021 dai an ƙiyasta cewa, kimanin gangar mai dubu 40 ne su ka tsiyaye daga wata tankar mai a yankin.
Kotun ƙolin ta tabbatar da hukuncin da kotunan baya su ka yanke, waɗanda su ka ce masu ƙorafin sun shigar da ƙarar ne bayan shuɗewar wa’adin shekaru shida da doka da tanada domin shigar da ƙara bayan aikata laifi.














































