Gwamnatin tarayya, ta ce za ta kashe naira biliyan 22 da
miliyan 400 wajen ciyar da Fursunoni a gidajen gyaran hali da
ke fadin Nijeriya a cikin shekara ta 2023.
Babban Sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida Dakta Shu’aib Belgore ya shaida hakan, a wani taron kwana biyu da aka shirya a kan hanyoyin da za a bi wajen rage cunkoson Fursunoni da garambawul ga hanyoyin gudanarwa da ke gudana a Abuja.
Belgore, ya ce an shigar da kudin a cikin kasafin shekara ta 2023, ya na mai cewa akwai yawan karuwar Fursunonin da ake fama da su a gidajen yarin Nijeriya, ta yadda kashi 80 cikin 100 su na zaman jiran shari’a ne.
Ya ce akwai gidajen yari 244 da ke dauke da Fursunoni dubu 75 da 507, lamarin da ya janyo da dama daga cikin su ke fama da cunkoso.














































