Home Labaru Na Fi Karfin Kujerar Ministan Abuja A Gwamnatin Tinubu

Na Fi Karfin Kujerar Ministan Abuja A Gwamnatin Tinubu

275
0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya ce ko an nada shi
Ministan Birnin Tarayya a karkashinGwamnatin Bola Tinubu
ba zai karba ba.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne, yayin da ake shirye-shiryen rabon mukamai a sabuwar gwamnatani, inda ake hasashen za a nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ko ministan Abuja.

Ya ce ko an ba shi ministan Abuja ba zai karba ba, domin akwai matasan su ka fi dacewa da kujerar.

Da ya ke jawabi a wajen taron kaddamar da wani littafi a Abuja, El’-Rufa’i ya ce ba zai koma gidan jiya ba, domintun da ya bar Abuja bai sake komawa ba sai a shekara ta 2016 da aka nada abokin karatun shi a matsayin minista ya bukaci ganin sa.

Gwamna El-Rufa’i ya kara da cewa, yanzu ya tsufa da fita yin rusau, don haka gara a samo matasa masu jini a jika, ya na mai cewa nan da kwana 19 zai bar Kaduna kuma ba zai kara zuwa ba sai idan ya zama dole.

Leave a Reply