Kotun Ƙoli ta sa ranar yanke hukuncin shari’ar cancantar takarar kujerar sanata tsakanin Bashir Machina da Sanata Ahmad Lawan.
A ranar Larabar da ta gabata ne, Kotun Ƙoli ta ce za ta yanke hukuncin a ranar 6 Ga watan Fabrairu, domin bayyana wanda ya cancanta ya tsaya wa APC takarar sanatan mazabar Yobe ta Tsakiya, tsakanin Bashir Machina da Shugaban Majalisar Dattawa sanata Ahmad Lawan.
Ahmad Lawan dai shi ke kan kujerar sanata, amma Machina ya kada shi a zaɓen fidda gwanin da aka yi.
A Cikin watan Nuwamba na shekara ta 2022 ne, Kotun Ɗaukaka Ƙara da keAbuja ta ƙara tabbatar wa Machina halascin takarar sa, yayin da Ahmed Lawan ya ce ya haƙura ba zai kai ƙara Kotun Ƙoli ba, amma APC ta ce ba ta haƙura ba sai ta garzaya Kotun Ƙoli.