Home Labaru Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar Secondus Ta Neman Dakatar Da Taron

Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar Secondus Ta Neman Dakatar Da Taron

12
0

Wata Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Fatakwal, ta yi watsi da ƙarar da tsohon shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya shigar ya na neman ta dakatar da babban taron jam’iyyar na ƙasa.

A cikin ƙarar da ya shigar, Secondus ya nemi kotun ta hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taron da ta shirya yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba na shekara ta 2021.

Daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun, Secondus ya nemi ta ba shi wuƙa da nama na aiwatar da babban taron.

Rahotanni sun ce, dukkan alƙalan kotun a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani, sun amince jam’iyyar PDP ta cigaba da shirin gudanar da taron, wanda a lokacin ne za ta zaɓi sabbin shugabannin ta na ƙasa a muƙamai daban-daban.