Wata kotu a jihar Katsina ta yanke wa wani mutum mai shekaru 70 mai suna Lawal Abdullahi Izala hukuncin daurin watanni 18 a gidan gyaran hali.
An dai kama Izala ne bisa zargin sa da zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari a makon da ya gabata.
Wata majiya ta ce, an gurfanar da Lawal Abdullahi da wasu mutane biyu a gaban kuliya a kan tuhumar su da furta kalaman da za su iya tada zaune tsaye.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Izala ya ce ya yi furucin ne a cikin fushi a lokacin da ya ziyarci kauyen su ya gano cewa ‘yan bindiga sun kashe wasu yan uwan sa sun kuma sace shanu 15.
A yayin zartar da hukuncin, alkalin kotun ya ce an samu Izala da laifukan assasa fitina da rashin da a ga hukuma, matakin da ya sa aka yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali a laifin farko, sai kuma na shekara guda na laifi na biyu.
A karshe alkalin ya ba Izala zabin biyan tara ta naira dubu 10 a laifin farko, da kuma naira dubu 20 a laifin na biyu, sai dai wasu mutane a jihar sun biya wa dattijon kudin tarar, lamarin da ya sa alkalin ya sake shi.
You must log in to post a comment.