Home Labaru Kotu Ta Karɓi Sakamakon Zaɓen Jihohi 17 Daga Hannun Peter Obi Domin...

Kotu Ta Karɓi Sakamakon Zaɓen Jihohi 17 Daga Hannun Peter Obi Domin Tantance Sahihancin Su

1
0

Dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi, ya gabatar wa Kotun
Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa sakamakon zaɓe
daga jihohi 17 da ya ke iƙirarin an yi masa maguɗi.

Peter Obi dai ya yi zargin cewa an yi masa maguɗi, kuma hukumar ya ke zargi da yin maguɗin, domin a cewar sa, hukumar ta karya dokar ƙasa da Dokar Zaɓe lokacin gudanar da zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ranar Talatar da ta gabata ne, lauyan Peter Obi Ben Anichebe ya gabatar wa kotu sakamakon zabubbuka daga jihohi 17, kuma duk sakamakon waɗanda aka sanya wa hannu ne daga mazaɓu.

Daga cikin sakamakon na jihohi 17, akwai sakamakon zaɓe daga ƙananan hukumomi 21 na Jihar Adamawa, da 23 daga jihar Bayelsa, da 21 daga jihar Benue, da 21 daga Jihar Kogi, da 11 daga jihar Nasarawa, da 25 na ƙananan hukumomin jihar Neja, da na ƙananan hukumomin Ondo 18, da 23 na ƙananan hukumomin jihar Sokoto.

Sauran sun hada da na ƙananan hukumomi 25 na jihar Delta, da 11 daga jihar Ekiti, da 25 na jihar Imo, da 21 daga ƙananan hukumomin jihar Kaduna, da kuma 27 na ƙananan hukimomin jihar Oyo.