Home Home KOTU Ta Karɓi Kwafen Takardun Zargin Asiwaju Ya Yi Harƙallar Muggan Ƙwayoyi

KOTU Ta Karɓi Kwafen Takardun Zargin Asiwaju Ya Yi Harƙallar Muggan Ƙwayoyi

1
0

Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ta karɓi kwafen takardun da ake kafa hujja da su cewa Shugaba Tinubu ya yi tu’ammali da miyagun ƙwayoyi har Amurka ta ci shi tarar dala dubu 460.

Kotun dai ta karɓi takardun ne a matsayin shaidu a ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi.

Peter Obi ya na ƙalubalantar nasarar Tinubu, inda ya ke neman kotu ta ayyana cewa shi ne ya ci zaɓe ko kuma a soke zaɓen a yi wani sabo, ya na mai ikirarin cewa an tafka maguɗi a lokacin zaɓe, kuma Tinubu bai cancanci tsayawa takarar zaɓe ba.

Obi dai ya kafa wa Kotun hujja ne daga dala dubu 460 da Kotun Gundumar Illinois ta ci Tinubu tara bayan an kama shi da miyagun ƙwayoyi a Amurka.

Haka kuma, Peter Obi ya ce takarar Kashim Shettima haramtacciya ce saboda ya fito takara wuri biyu a lokaci guda.