Wata Babbar Kotu da ke zama a Abuja, ta ce daga yanzu ta
haramta wa Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta
Ƙasa NBC ta ci gidajen rediyo da talabijin da ke faɗin
Nijeriya tara.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne a zaman sauraren shari’ar da ta yi a ranar Larabar nan.
Da yake yanke huncin, Mai Shari’a James Omotosho ya yi watsi da tarar Naira dubu 500 da NBC ta yanka wa tashohi 45 ranar 1 ga Maris na shekara ta 2019 a matsayin horo bisa aikata ba daidai ba.
Alƙalin ya kara da cewa, Dokar NBC da ta ba hukumar damar yanka tara ta ci karo da Sashe na 6 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da ya ba da ikon shari’a a kotun shari’a, don haka ya ce kotu ba za ta zuba ido wata hukuma ta na cin tara ba tare da bin doka ba.














































