Home Labaru Kotu Ta Haɗe Ƙararrakin Da Jam’Iyyu Ke Ƙalubalantar Nasarar Tinubu

Kotu Ta Haɗe Ƙararrakin Da Jam’Iyyu Ke Ƙalubalantar Nasarar Tinubu

1
0

Kotun sauraren ƙararrakin zaben shugaban kasa, ta hade
kararraki uku da ‘yan hamayya su ka shigar a kan sakamakon
zaben da hukumar zabe ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar
APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Wadanda suka shigar da kararrakin sun hada da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, da kuma Peter Obi da jam’iyyar sa ta Labour sai kuma jam’iyyar APM.

A rahoton da kotun mai alkalai biyar ta fitar karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani, ta umarci a fara sauraren korafin su Peter obi da jam’iyyar sa ta Labour a ranar 30 ga watan Mayu.

Kotun, ta umarci masu kara su gabatar da korafe-korafen su a cikin makonni uku, wanda a lokacin za ta kira masu gabatar da shaidar da aka ware guda 50 daga ranar 30 ga watan na Mayu, yayin da masu korafin za su fara kiran masu shaida a kuma kammala a ranar 23 ga watan Yuni.

Ta ce za a kammala shari’ar a ranar 5 ga watan Agusta, lokacin da lauyoyn masu kara za su gabatar da jawaban su na karshe a rubuce, daga nan kuma kotun za ta ware ranar da za ta bayyana hukuncin ta.