Home Labaru Shugaba Biden Ya Bayyana Wakilan Amurka Da Za Su Halarci Rantsar Da...

Shugaba Biden Ya Bayyana Wakilan Amurka Da Za Su Halarci Rantsar Da Tinubu

1
0

Shugaba Joe Biden na Amurka, ya bayyana sunayen wakilan
gwamnatin shi da za su halarci bikin rantsar da sabon
shugaban Nijeriya Bola Tinubu a Abuja.

A cikin wata sanarwa da Biden ya wallafa a shafin sa na yanar gizo, shugaban ya sanar da tawagar mutane tara da za su halarci taron, a karkashin jagorancin Ministar Gidaje da Raya Birane ta Amurka Marcia L. Fudge.

Ana sa ran halartar tsofaffin shugabannin kasashen duniya da wadanda ke kan mulki da jami’an diflomasiyya da shugabannin hukumomin duniya da wakilan gwamnatocin kasashe.

Za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya na 16, a ranar ta 29 ga watan Mayu a dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja.