Home Labaru Kotu Ta Bayar Da Belin Abba Kyari Kan Miliyan 50

Kotu Ta Bayar Da Belin Abba Kyari Kan Miliyan 50

87
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bada belin
dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba
Kyari a kan kudi naira miliyan 50 bisa tuhumar da ake yi
masa da ‘yan’uwan sa biyu a kan zargin kin bayyana wa
hukumar NDLEA kadarorin su.

Hukumar NDLEA dai ta shigar da tuhume-tuhume 24 masu a kan Abba Kyari da ‘yan’uwansa biyu, wadan su ka hada da wani Mohammed Baba Kyari da Ali Kyari da aka gurfanar da a watan da ya gabata.

Da ya ke zartar da hukunci, mai shari’a James Omotosho ya bada belin Abba Kyari bisa sharadin biyan naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya ma shi.

Mai shari’a Omotosho ya kara da cewa, ya zama dole wadanda za su tsaya wa Abba Kyari su kasance sun mallaki kadarar da ta kai naira miliyan 25 a karkashin ikon shari’a da sauran sharudda.

Ya ce ko da Abba Kyari ya cika sharuddan belin, yarda da sakin sa ya ta’allaka ne a kan ci-gaba a shari’ar da ake yi da shi a kan wasu zarge-zarge hudu da ake yi masa game da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Leave a Reply