Home Labaru Wasu Na Ƙorafi, NNPP Na Dariya Da Shugabancin Majalisar Najeriya

Wasu Na Ƙorafi, NNPP Na Dariya Da Shugabancin Majalisar Najeriya

323
0

Ra’ayoyi sun bambanta, musamman tsakanin jam’iyyun siyasa
bayan an fitar da manyan jami’an Majalisar Tarayya ta goma.

Sa’o’I kadan bayan sanar da jagororin, jam’iyyun APC da PDP da su ka mamaye majalisun biyu, sun nuna rashin jin daɗi da sunayen da aka fitar a Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

Jam’iyyar APC ce ke da kujeru takwas na ɓangaren masu rinjaye, inda Sanata Opeyemi Bamidele ya samu matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.

PDP kuma ta tashi da kujeru huɗu, wadanda su ka hada da ta shugaban marasa rinjaye a dukka majalisun biyu da mataimakin shugaban marasa rinjaye a majaisar dattawa da kujerar mai tsawatarwa na majalisar wakilai.

Jami’yyun Labour da NNPP kuma sun raba kujeru huɗu na ɓangaren marasa rinjaye, inda a majalisar dattawa jam’iyyar Labour ta samu kujerar mai tsawatarwa da mataimakin mai tsawatarwa a majalisar wakilai, yayin da NNPP ta samu kujerar mataimakin shugaban marasa rinjaye, amma a majalisar dattawa ta samu mataimakin mai tsawatarwa.

Leave a Reply