Home Labaru Kotu Ta Bada Belin Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya A Kano

Kotu Ta Bada Belin Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya A Kano

33
0

Kotu ta bada belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya.

Rahotanni sun ce, Kotun ta ba da belin ne a kan naira miliyan daya, tare da gindaya ma shi wasu sharuda da sai ya cika sannan belin zai tabbata.

Mai shari’a Aminu Gabari, ya ce bayan biyan kudin da Dan Sarauniya zai yi sai kuma ya ajiye fasfo din sa na tafiya, sannan zai kai mutane biyu da za su tsaya ma shi, wadanda dole na farko ya kasance mai garin kauyen Sarauniya, yayin da na biyun kuma dole zai kasance limamin garin su ko kuma kwamandan Hizba na garin.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne ‘yan sanda su ka kama Injiniya Mu’azu a Abuja, daga baya aka maida shi Kano aka gabatar ma shi da tuhume-tuhumen da ake zargin sa na keta mutuncin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.