Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe, ta ɗage sauraren ƙarar da
jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta na shugaban ƙasa Atiku
Abubakar su ka shigar a kan nasarar da Bola Tinubu ya samu.
Yayin zaman kotun a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani, Kotun ta ɗage ci-gaba da sararen ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Mayu 2023.
A Ƙorafin da su ka shigar dai, jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su na ƙalubalantar bayyana Tinubu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an ga Atiku Abubakar da kansa ya halarci zaman kotun na ranar Alhamis din nan a Abuja.














































