Home Labaru Kotu Ta Ƙwace Tulin Dukiyar Katafaren Ɗan Damfara Okeke

Kotu Ta Ƙwace Tulin Dukiyar Katafaren Ɗan Damfara Okeke

14
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ta ƙwace illahirin kuɗaɗe da gidaje da motocin da kasurgumin ɗan damfara Obinwanne Okeke ya mallaka a Nijeriya.

Yanzu haka dai, Okeke ya na zaman kurkuku na tsawon shekaru 10 a kasar Amurka, bayan an same shi da laifin damfarar mutane Dala miliyan 11.

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya ba hukumar EFCC umarnin, bayan da lauyan EFCC Chinenye Okezie ya roƙi kotu ta ƙwace kadarorin.

Daga cikin kadarorin da aka ƙwace, akwai Gida mai lamba 4 da ke Rukunin Gidajen Oakville, gida mai ɗakuna 5 a Rukunin Gidaje na Standard Estate duk a Abuja, sannan an ƙwace duk wasu kayan al’atu da ke cikin gidajen.

Haka kuma, an ƙwace wasu motocin alfarma masu tsada guda biyu ƙirar Toyota, bayan tun farko ya miƙa wa Gwamnatin Tarayya Naira miliyan 280, da wasu Naira miliyan 240 da kuma Naira miliyan 40.

Lauyan EFCC, ya ce za a saida gidajen a haɗa da kuɗaɗen duk a biya waɗanda ya damfara a kasar Amurka.