Home Labaru Kotu Ta Ƙwace Naira Miliyan 775 Da Gidaje Daga Tsohon Akanta Janar...

Kotu Ta Ƙwace Naira Miliyan 775 Da Gidaje Daga Tsohon Akanta Janar Da Hadimin Dasuƙi

26
0

Babbar Kotun Tarayya ta ƙwace jimillar naira miliyan 775 da wasu gidaje uku daga tsohon babban Akantan Tarayya Jonah Otunla da Bello Fadile, tsohon hadimin Sambo Dasuƙi ne.

Wasu daga cikin kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da gida mai Lamba 8, a Ajayi Crowther Street da ke Asokoro a Abuja, da wani fili a yankin Cadestral Zone da ke Maitama a Abuja.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ce ta fitar da sanarwar kwace kadarorin.

Sauran kadarorin sun hada da wani Otal da ake kan gininwa a fili da ke Gwarimpa a Abuja, da wani gida mai ɗaki 4 duk a Gwarimpa da ke binin Abuja.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ya ce Mai Shari’a D.U Okorowo ne ya yanke hukuncin, ya na mai cewa tuni kotu ta gamsu da cewa an gina gidajen ne da kuɗaɗen sata da harƙalla.

Mai Shari’a Okorowo ne ya bada umarnin ƙwace kadarorin da kuɗaɗen baki ɗaya, bayan hukumar EFCC ta shigar da ƙarar neman a ƙwace dukiyoyin.