Home Labaru Ilimi Koshin Lafiya: Samuel Kalu Ya Warke Bayan Faduwa A Filin Wasa

Koshin Lafiya: Samuel Kalu Ya Warke Bayan Faduwa A Filin Wasa

42
0
Samuel Kalu

Dan kwallon Bordeaux, Samuel Kalu ya murmure, bayan da ya fadi a cikin filin Stade Velodrome a karawar da suka yi 2-2 da Marseille ranar Lahadi in ji abokin wasan sa Remy Oudin.

Dan Najeriya, mai shekara 23, ya samu agajin gaggawa a lokacin da ya fadi a cikin filin a minti na shida da fara wasa.

Ya mike da kafafunsa minti daya tsakani, sannan ya rike jakar kankara da ya kara a kan sa.

Kalu ya ci gaba da wasa, amma daga baya aka sauya shi, bayan da aka fuskanci jiri na jan shi.

Kalu ya taba faduwa a fili sakamakon yanayin zafi a lokacin atisaye a Najeriya a shirin gasar Afirka a 2019