Home Labaru Matsalar Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-Zangar Lumana A ’Yantumaki Dake Jihar Katsina

Matsalar Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-Zangar Lumana A ’Yantumaki Dake Jihar Katsina

58
0
Zanga-Zangan Katsina

Da safiyar ranar Litinin ne wasu fusatattun matasa suka rufe babban titin Katsina zuwa Kankara a garin ’Yantumaki don nuna bacin ran su kan yadda sha’anin tsaro yake kara tabarbarewa a yankin.

Matasan, wadanda suka rika kone tayoyi tare da tare motoci sun yi kira ga gwamnati ta dauki mataki don kare lafiya da dukiyoyin jama’ar kauyukan da suke kewaye da garin, wanda suka ce ’yan bindiga sun addabe su da kisa da kuma satar dabbobi.

Da yake wa Aminiya karin bayani, wani matashi mai suna Danladi, ya bayyana cewa lamarin rashin tsaro na kara kamari a yankin, inda a kullum sai maharan sun shiga kauyukan su sun kashe mutane tare da sace masu dabbobi.

Yace ko a daren jiya sai da suka share fiye da sa’o’i uku a kauyen Amarawa inda suka kashe mutum biyu da jikkata da dama tare da kore dabbobin garin kaf.

Ya ci gaba da cewa A halin yanzu garin ’Yantumaki cike yake makil da ’yan gudun hijira wadanda suka baro kauyukan su, musamman daga gabashin garin.

Matashin ya tabbatar wa Aminiya zargin da yake wa jami’an soja a garin na rashin kai dauki ga jama’a duk kuwa da cewa ana kokarin sanar da su a yayin da maharan ke cin Karen su ba babbaka a kauyukan.